Ferguson ya janye kauracewar da ya yiwa BBC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya yarda da hanye kauracewa hira da ya keyi da BBC.

Ferguson dai ya fara kauracewa gidan yadda labari na BBC ne tun a shekarar 2004, bayan BBC ta yadda wani shiri kan dan sa, Jason.

A wata sanarwa da ya fitar: "Sir Alex da BBC sun kawarda duk wani banbance banbancen dake tsakaninsu, wanda kuma ya sa ya kauracewa shirye shiryen, gidan yadda labaran."

United dai za ta kara ne da Arsenal a filin Old Trafford a ranar Lahadi.

Janye kauracewar da Sir Alex Ferguson din ya yi, ya biyo bayan tattaunawar da yi da Direkta Janar din BBC Mark Thompson.