CAS za ta saurari karar Amos Adamu

Image caption Amos Adamu

Kotun daukaka kara ta wasanni wato CAS ta ce za ta saurari karar da tsohon jami'in kwamitin gudanarwa na Fifa, wato Amos Adamu ya shigar mata.

Fifa dai ta dakatar da Amos Adamu ne na tsawon shekaru uku daga harkar kwallon kafa saboda ana zarginsa da neman cin hanci.

Kotun za ta saurari karar ne a ranar 4 ga watan Okutoba.

Adamu ne jami'in Fifa na farko da aka ladabtar saboda zargin neman karbar cin hanci da wata jaridar Ingila ta buga.

Jaridar dai ta zargi Adamu ne da neman cin hanci kafin ya kada kuri'a kan kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekarar 2018 da 2022.