An hana Bolt shiga tseren mita 100

Image caption Usain Bolt

An hana dan tseren Jamaica, Usain Bolt shiga tseren karshe na mita 100 a gasar tsalle-tsalle da guje guje ta duniya da ake yi a birnin Deagu a kasar Koriya ta kudu.

Dan uwansa dan kasar Jamaica Yohan Blake ne ya lashe kyautar zinari a tseren.

Bolt mai kare kambunsa a gasar ya fara tseren ne kafin a bukaci 'yan tseren sun fara, abun da kuma ya sa aka hana shi shiga tseren.

Blake ya lashe tseren ne cikin dakikai 9.92 .

A yanzu haka dai tseren mita dari biyu ne da na 4x100 su ka ragewa Bolt a gasar.