Manchester City ta lallasa Tottenham da ci biyar da nema

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tottenham vs Manchester City

Edin Dzeko ya zura kwallaye hudu, inda ya taimakawa Manchester City a haskakawar da takeyi a gasar Premier.

Manchester City dai ta lallasa Tottenham ne a gidanta da ci biyar da guda abun da kuma yasa ta dare kan tebur a gasar Premier

Sergio Aguero ya zura kwallo guda shima a wasan a yayinda kuma Younes Kaboul ya fanshewa Tottenham kwallo guda.

Bayaga kwallayen da Manchester City ta zura a wasan ta shafa Tottenham sosai a wasan.