Didier Drogba ya fara murmurewa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Didier Drogba a gadon marasa lafiya

Didier Drogba ya fara murmurewa a asibiti, bayan raunin da ya samu a wasan da Chelsea ta doke Norwich da ci uku da guda a gasar Premier ta Ingila.

Chelsea ta ce jami'an lafiyarta za su ci gaba da duba lafiyar dan wasan mai shekarun haihuwa 33 domin su san irin halin da yake ciki.

Mai tsaron gidan Norwich, John Ruddy ne ya naushe kan Drogba inda kuma ya yi mumunar faduwa.

An dai fidda dan wasan ne akan gadon daukar marasa lafiya a yayinda aka sanya mishi na'urar namfashi.

Bayan wasan dai kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce: "Likitocin sun yi kokarin akansa, kuma yana murmurewa."