Lampard na da kwarin gwiwa akan Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Frank Lampard

Dan wasan Chelsea Frank Lampard ya ce yana da kwarin gwiwa Chelsea za ta lashe gasar Premie a bana duk da irin rawar da United da City ke takawa yanzu a gasar.

Chelsea dai ta fuskanci matsaloli a wasanni biyu da ta lashe sannan kuma ta buga canjaras a guda, abun da wasu kuma ke ganin cewa akwai shakku kan kungiyar a kakar wasan bana.

"Yanzu aka fara kakar wasa bamu gama murmurewa bane." In ji Lampard.

A yanzu haka dai Chelsea na maki biyu ne bayan City da United.

Lampard ya ce nan daba yana ganin Chelsea za ta ba mutane mamaki.