'A gaskiya an kaskantar da mu'- Wenger

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce yaji matukar kunya bayan da kungiyarshi ta sha kashi a hannun Manchester United da ci takwas da biyu.

Wayne Rooney ya zura kwallaye uku a wasan, a yayinda a yanzu haka kuma Manchester United ke jagoranci akan tebur a gasar Premier, saboda kwallayen da ta zura.

"Dolene kaji kunya idan aka zurama kwallaye takwas." In ji Wenger.

"A gaskiya an kaskantar da mu."

Shiko Sir Alex Ferguson cewa ya yi: "Arsenal ba kawan lasa bace. Za ta taka rawar gani idan manyan 'yan wasanta su ka dawo".

Wenger ya ce na kokarin siyan 'yan wasa kafin wa'adin siyan 'yan wasa ya cika a ranar 31 ga wannan wata, domin maye gurbin Fabregas da Nasri da su ka bar kungiyar.

Wenger, dai ya nace cewa ba zai ajiye aikinsa ba.