Joe Cole na shirin komawa Lille na wucin gadi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joe Cole

Dan wasan Liverpool Joe Cole na tattaunawa da Kungiyar Lille ta Faransa da zumar komawa kungiyar a kakar wasan bana na wucin gadi.

Kungiyar Queens Park Rangers da Tottenham Hotspur ma sun nuna sha'awarsu na siyan dan wasan mai shekarun haihuwa 29.

Cole dai koma Liverpool ne daga Chelsea a watan Yulin shekarar 2010, inda ya sa hannu a kwantaragi na tsawon shekaru hudu.

Dan wasan dai ya farawa Liverpool wasa 11 ne a kakar wasan bara inda kuma aka sallame shi a wasan farko daya bugawa kungiyar.

Lille dai za ta buga gasar zakarun Turai a bana, bayan ta lashe gasar Faransa a karon farko tun shekarar 1954.

Cole bai ma samu zama a benci ba a wasanni ukun da Liverpool ta buga a kakar wasan bana a gasar Premier.