Liverpool ta sayi Sebastian Coates

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sebastian Coates

Liverpool ta kammala siyan dan wasan bayan kasar Uruguay, Sebastian Coates daga Nacional.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 20, ya taka rawar gani ne a lokacin da ya takawa Uruguay leda a gasar Copa America da aka yi a watan Yulin.

Coates shine dan wasa na shida da Liverpool ta siya a kakar wasan bana.

Dan wasan a yanzu haka ya hadu ne da dan kasarsa dake takawa Liverpool leda wato Luis Suarez.