Scott Parker ya koma Tottenham

Image caption Scott Parker

Tottenham ta sayi Scott Parker daga West Ham akan fam miliyan biyar.

Dan wasan ne dai ya mika takardun cewa yana so ya bar kungiyar domin taka leda a gasar Premier.

Zuwa Parker Tottenham zai iya sa kungiyar ta siyarwa Stoke City Wilson Palacios, bayan ta dade tana zawarcin dan wasan.

Sai dai kuma Tottenham ta bayyana cewa David Bentley zai koma West Ham din na wucin gadi a kakar wasan bana.