Arsenal ta sayi Mikel Arteta daga Everton

Mikel Arteta
Image caption Cinkin Mikel Arteta ya bayar da mamaki

Arsenal ta sayi Mikel Arteta daga Everton a ranar karshe ta musayar 'yan wasa a kakar bana, yayin da Chelsea ta sayi Raul Meireles daga Liverpool.

Arsenal ta kuma karbi aron dan wasan tsakiya na Chelsea Yossi Benayoun.

A cewar masu sharhi kan al'amuran tattalin arziki Deloitte, sayayyar da kulob-lukan Premier ta Ingila suka yi ya kai fan miliyan 485.

Hakan na nufin an samu karin kashi 33 cikin dari idan aka kwatanta da abinda aka kashe bara, inda aka samu karin fan miliyan 120.

Arsenal ta kuma dauki dan wasan baya na Jamus Per Mertesacker da kuma Andre Santos daga Fenerbahce, a kokarin da Arsene Wenger ke yi na farfado da kimarsa bayan da suka sha kashi da ci 8-2 a hannun Man United.

Manchester City ma ta dauki tsohon dan wasan Manchester United Owen Hargreaves a kyauta, yayin da Craig Bellamy ya koma tsohon kulob dinsa wato Liverpool.

Karin 'yan wasa biyu kuma sun bar Liverpool, inda Joe Cole ya koma zakarun Faransa Lille a matsayin aro na shekara guda, sai Christian Poulsen da ya koma Evian.