Capello ya jinjinawa tawagar Ingila

Fabio Capello
Image caption Yanzu Ingila ta yi kane-kane a saman teburin rukunin G

Kocin Ingila Fabio Capello ya jinjinawa 'yan wasanshi bayan da suka lallasa Bulgaria da ci 3-0 a wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2012.

Gary Cahill ne ya fara zira kwallon farko, kafin Wayne Rooney ya kammala aikin da kwallaye biyu, abinda kuma ya baiwa Ingila damar yin kane-kane a saman teburin rukunin G.

"Yana da matukar muhimancin mu yi nasara a nan," A cewar Capello.

"Mun taka rawar gani sosai, amma ba wasa ne mai sauki ba. Mun zira kwallaye masu kyau, kuma mun taka leda a baki dayan wasan."

"Na yi murna da rukunin, da ma yadda 'yan wasan suka nuna hazaka."

Kocin ya kuma yabawa rawar da 'yan wasan suka taka, musamman Ashley Young, wanda ya rinka taimakawa Wyane Rooney da kuma sauran 'yan gaban.

"Young ya buga a mataki daban bara a Aston Villa, amma yanzu tunda ga Stewart Downing, za mu iya sauya su a lokuta da dama," kamar yadda Capello ya bayyana.