Capello ya gargadi Lampard

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Engila Fabio Capello

Kocin Ingila Fabio Capello ya gargadi Frank Lampard da sauran manyan 'yan wasan Ingila cewa ba su da tabbas din samun wuri a tawagar kwallon kasar.

Lampard, mai shekaru 33, ya fara wasan da Ingila ta doke Bulgaria da ci 3-0 a ranar Juma'a a benci, inda kocin ya sanya Gareth Barry a maimakonsa.

"Lampard na daya daga cikin manyan 'yan wasan tsakiya na Ingila, amma a cewar Capello.

"Wasanni biyu da ya buga a bana ba su kayatarba, kuma a yanzu Barry ne ke haskakawa. Akwai bukatar 'yan wasana su amince da matakan da zan dauka."

Capello ya gwammace fara wasan ba tare da Lampard ba, duk da cewa Steven Gerrard da Jack Wilshere na fama da rauni.

Hakan na nufin wannan ne karo na farko cikin shekaru tara da Ingila ta fara wasa ba tare da Lampard ko Gerrard ba.