Anichebe ya samu rauni a wasan Najeriya

Image caption Victor Anichebe

Dan wasan Everton Victor Anichebe ba zai taka leda ba na tsawon makwanni uku bayan raunin da ya samu a wasan da Najeriya ta buga da Madagascar a karshen mako.

Anichebe dai ya samu raunin ne a yayinda aka kusan kammala wasan da Najeriya ta yi galaba da ci biyu da nema.

A yanzu haka dai ya koma Burtaniya ne domin ya yi jinya, a yayinda abokan wasansa suka nufi Bangladesh domin karawa da Argentina a wasan sada zumunci a ranar Talata.

Kocin Najeriya, Samson Siasia ya soki yadda filin wasa na Antananarivo a Madagascar ya lallace.