Lampard zai taka rawar gani - Capello

Image caption Frank Lampard

Kocin tawagar Ingila, Fabio Capello ya ce har yanzu Frank Lampard na da muhimmiyar rawar da zai taka a tawagar Ingila.

Capello dai ya ajiye Lampard ne a benci a wasan da kasar ta buga da Bulgaria a ranar asabar.

Capello ya ce Lampard, mai shekarun haihuwa 33, zai iya taka leda a wasa da Wales a ranar Talata.

"A shirye yake ya taka mana leda, yana daya daga cikin manyan 'yan wasan mu." In ji Capello.