US Open: Murray ya kai zagaye na hudu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Andy Murray

Andy Murray ya kai zagayen 'yan wasa goma sha shida na karshe a gasar US Open bayan ya doke Feliciano Lopez.

Dan kasar Burtaniya din ya lashe wasanni biyar a jere da ya buga da Lopez a baya.

Murray, mai shekarun haihuwa 24, ya mamaye wasan gabaki daya.

A yanzu haka dai zai buga da Donald Young a zagaye na hudu, bayan da wasan ya doke sa a farkon wannan shekara.