Petr Cech ya dawo horo bayan rauni

Image caption Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech

Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech ya yi bazata ya dawo horo, bayan raunin da ya samu a gwiwarsa.

A baya dai ana ganin dan wasan mai shekarun haihuwa 29 ba zai taka leda ba na tsawon makwanni hudu saboda raunin da ya samu a gwiwarsa a watan daya gabata.

A yanzu haka dai Cech, ya murmure, kuma akwai yiwuwar dan wasan ya taka leda a wasan da Chelsea za ta buga da Sunderland a karshen mako.

Ba'a dai zura kwallo a ragar Chelsea ba a kakar wasan bana, kafin Cech ya samu rauni.