Vermaelen zai yi jinya na mako guda

Image caption Thomas Vermaelen

Dan wasan Arsenal, Thomas Vermaelen zai yi jinya na tsawon wata guda bayan aikin tiyatar da aka yi mishi a idon sahunsa.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25 ya samu rauni ne a wasan da Arsenal ta buga da Udinese a gasar zakarun Turai.

Wannan dai wani babban komawa baya ne ga Arsenal din, wanda ke fusktar matsalolin rashin manyan 'yan wasanta saboda rauni.

Jack Wilshere ma zai yi jinya na tsawon watanni uku.

Vermaelen dai bai buga wasa sosai a kakar wasan bara ba saboda ya yi jinyar rauni.