'Kungiyoyi da dama na iya lashe gasar Premier'- Ferguson

Image caption Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce kungiyoyi biyar ko shida ne za su yi takarar lashe gasar Premier a bana.

"Akwai matukar wuya kungiya ta lashe gasar, saboda irin manyan kungiyoyin da ke kungiyar, kamarsu Arsenal da Tottenham da Chelsea sannan kuma ga irin su Manchester City da kuma Liverpool." In ji Ferguson.

Ferguson dai ya sayi wasu 'yan wasa a kakar wasan bana domin karfafa kungiyarsa.

"Idan kana kokarin lashe gasar, dolene kuma ka sayi 'yan wasan da zasu gina kungiyar kuma su rika taka leda na wasu 'yan shekaru."