Nijar ba za ta rufe iyakarta da Libya ba

Muhammadu Issofou
Image caption Da alamu shugaban Nijar Muhammadu Issofou na cikin tsaka mai wuya

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ya ce kasar ba za ta iya rufe iyakarta da Libya ba domin hana Kanal Gaddafi tsallakawa kasar ba.

Ministan Mohamed Bazoum ya shaida wa BBC cewa Kanal Gaddafi bai tsallaka iyaka zuwa kasarba ko kuma bai nemi yin hakan ba.

Ya ce magoya bayan Gaddafi da suka shiga Niamy babban birnin Nijar, na da ikon zama ko kuma ficewa daga kasar.

Majalisar wucin gadi na Libya sun ce suna neman goyon bayan Nijar domin hana Gaddafi shiga kasar.

Jagoran siyasa na Majalisar Fathi Baja ya ce Majalisar ta NTC, ya ce sun aika tawaga zuwa Nijar domin "tabbatar da tsaro a kan iyakokinmu da kuma hana Gaddafi da dakarunsa ko iyalansa shiga kasar Nijar din".

Da aka tambaye shi ko Nijar za ta rufe iyakarta, Mr Bazoum ya ce: "Ba mu da karfin ikon rufe iyakar....tana da girma sosai, ga kuma karancin kayan aiki." Ya ce yana fatan Kanal Gaddafi ba zai nemi shiga kasar ba, amma Nijar bata yanke hukunci kan ko za ta karbe shi ba - ko kuma za ta mika shi zuwa kotun shari'ar laifuka ta duniya (ICC) - idan ya shiga kasar.

ICC na neman Kanal Gaddafi da dansa Saif al-Islam, da kuma tsohon shugaban leken asirinsa Abdullah Sanoussi.

Jami'ai a Nijar sun ce shugaban tsaron cikin gida na Gaddafi Mansour Daw, na daga cikin wadanda suka shiga kasar ranar Lahadi.

Matar Kanal Gaddafi, biyu daga cikin 'ya'yansa maza da kuma mace daya sun tsere zuwa Algeria a makon da ya gabata.

Har yanzu dai babu tabbas kan inda Kanal Gaddafin ya ke.