Dalglish ya kare Andy Carroll

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya kare Andy Carroll bayan sukar da kocin Ingila da Fabio Capello ya yiwa dan wasan game da rayuwarsa.

An dai sauya Carroll a wasan da Ingila ta yi akan Wales.

Capello dai ya ce idan dan wasan na son ya zama kwararre dolene dan wasan ya rage yadda yake shan giya.

Amma Dalglish ya nace cewa: "Babu abun da ya samu dan wasan kuma yana da kuzari kamar wani kowanni dan wasan.

"Ina ganin bai kamata ana cece kuce game yadda dan wasan ke tafiyarda rayuwarsa ba."

Kocin Liverpool din ya kara da cewa: "Andy bai taka rawar gani ba a kakar wasan bara saboda raunin da ya samu a gwiwarsa.

"Muna matukar farin ciki da cewa dan wasan ya dawo da kwarin gwiwa a kakar wasa ta bana saboda ya murmure."