Paul Ince ya soki tawagar kwallon Ingila

Paul Ince
Image caption Paul Ince ya taka rawar gani sosai a Ingila

Tsohon dan wasan Ingila Paul Ince ya soki tawagar kwallon kasar, yana mai cewa 'yan wasan ba sa daukar cewa dama ce suka samu ta bugawa kasar wasa.

"Muna ba su damar buga wasa haka kawai ba tare da cancanta ba," kamar yadda Ince ya shaida wa BBC Radio 5 live.

"A baya takawa Ingila leda ita ce babbar nasara a rayuwarka. Yanzu ba haka lamarin yake ba saboda akwai gasar zakarun Turai da kuma Premier."

Kalaman na tsohon kyaftin din Ingila na zuwa ne bayan da Ingila ta sha da kyar a hannun Wales da ci 1-0 a Wembley ranar Talata.

Tsohon dan wasan na Manchester United da Inter Milan, ya ce 'yan wasan na da laifi inda suke bayar da uzuri a lokacin da ya kamata su takawa kasarsu leda.

"Da zarar an kira ka, fatanka shi ne kaje ka taka leda. Amma yanzu akwai masu bayar da uzuri - na cewa suna da rauni, ba su da lafiya - domin kawai su samu damar takawa kulob dinsu leda a karshen mako".