Saboda Bruce na koma Sunderland - Bendtner

Nicklas Bendtner
Image caption Nicklas Bendtner ya taka rawa a Arsenal

Nicklas Bendtner ya ce karsashin aiki karkashin kocin Sunderland Steve Bruce ne ya sa shi yanke shawarar komawa kulob din.

Dan wasan, wanda ke taka leda a gaba, ya buga wasa karkashin Bruce a Birmingham tsakanin shekara ta 2006 - 07, ya koma Sunderland ne na wucin gadi.

"Wannan lokaci ne da na dade ina jira," dan wasan mai shekaru 23 ya shaida wa shafin intanet na Sunderland. "Steve Bruce shi ne babban dalilin da ya sa na dawo nan.

"Wannan ba karamar dama ba ce. Dama ce domin na farfado da rayuwar kwallo ta."

Bendtner ya koma Arsenal ne bayan ya taimakawa Birmingham ta samu damar komawa matakin Premier a kakar 2006-07.

Sai dai dan wasan na Denmark wanda ya zira kwallaye biyu a wasan da kasar ta doke Norway a wasan share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Turai ranar Talata, ya koma zaman benci a Arsenal din.