Ferguson ya soki tadewar da aka yiwa Cleverly

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya soki yadda dan wasan Bolton Kevin Davies ya tade Tom Cleverley abun kuma yasa dan wasan ya samu rauni.

An dai sauya Cleverley ne kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan da Manchester ta lallasa Bolton da ci biyar da nema a filin wasa na Reebok.

Kyaftin din Bolton Davies ne yayi sanadiyar sauya Cleverly saboda munmunar tadewar da ya yi masa.

Ba'a kuma gargadi Davies ba a lokacin amma daga baya ya sake tade Patrice Evra inda aka nuna mishi katin gargadi na dari a gasar Premier.

Ferguson dai ya ce zai duba yanayin tawagarsa kafin su garzaya Portugal inda za su fafata da Benfica a gasar zakarun Turai a ranar Laraba.