Mancini ya ce dolene City ta zage damtse

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya ce dolene City ta zage damtse duk da nasarar da kungiyar ta samu akan Wigan a filin wasan na Etihad.

Sergio Aguero ne ya zura kwallaye uku a wasan a yayinda shi kuma Carlos Tevez ya barar da fenarity.

A yanzu haka dai, City ta zura kwallaye 15 a wasanni hudu da ta buga a gasar Premier a kakar wasan bana.

Amma Mancini dai bai ji dadin yadda 'yan wasansa suka rika bare-baren kwallaye a wasan ba.

"Mun samu dama 15 kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma kwallo guda kawai muka zura, akwai matsala saboda wasa zai iya sauyawa yadda baka za ta ba." In ji Mancini.

"Kamata yayi tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ace mu riga mun lashe wasan. Dolene mu zage damtse."

A yanzu haka dai Aguero ya zura kwallaye shida a kakar wasan bana.