An bukaci Torres da ya yi bayani kan hirar da ya yi

Image caption Torres yana horo a Cheslea

Kungiyar Chelsea, ta bukaci Fernando Torres da yi mata karin haske game da wata hira da yayi da wani shafin Intanet inda ya soki yadda abokan wasansa ke taka leda.

Torres, dai yayi hira da shafin intanet na laliga ne da harshe Spaniya, inda kuma aka fasara kalamunsa a shafinsa na kansa da Turanci.

A hirar da Torres ya yi da shafin na Intanet ya soki abokan 'yan wasansa da rashin kuzari saboda sun tsufa.

Dan wasan dai ya musanta kalaman nasa inda yace ba'a fasara kalamunsa daidai ba.

Harwa yau Chelsea, ta bukaci da a bata ainahin hirar da yayi ba wanda aka fasara ba.

Chelsea dai ta ce ita ta ba Torres hurumin hira da shafin intanet din, kuma ba za ta hukunta shi ba saboda ya yi hira da su.

Kocin kungiyar Andre Villas Boas ya ce kungiyar naso ta san sahihin abun da dan wasan ya ce ne domin ta tattauna da shi.