Kwallon kwando: Tawagar mata ta Senegal ta lashe zinari

Hakkin mallakar hoto google
Image caption yar wasan Senegal

Tawagar mata ta Senegal ta lashe zinari a wasan karshen kwallon kwado da aka buga a gasar wasanni ta Afrika da ake yi a birnin Maputo na kasar Mozambique.

Senegal din dai ta doke Angola ne da maki 64-57.

Sai kuma wasan lashe tagulla inda Najeriya ta yi galaba akan mai masaukin baki Mozambique da maki 72-76.

A wasan zagaye na farko, Mozambique din ta yi galaba akan Najeriya.

Senegal dai ce ta fidda Najeriya a wasan kusa dana karshe a wasan kwallon kwando a gasar.