Novak Djokovic ya lashe US Open

Novak Djokovic Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Novak Djokovic ya lashe Grand Slam uku a bana

Novak Djokovic ya tabbatar da matsayinsa na jagora a fagen Tennis din maza bayan da ya doke Rafael Nadal inda ya lashe gasar cin kofin US Open.

Dan wasan wanda shi ne na daya a jerin wadanda suka shiga gasar ya lashe wasanne da ci 6-2 6-4 6-7 (3-7) 6-1 a sa'o'i hudu da minti goma.

Nadal, wanda ke kokarin lashe Grand Slam a karo na 11, a yanzu ya sha kayi a dukkan wasanni shida da ya kara da Djokovic a 2011.

A yanzu Djokovic ne ke rike da kofunan Australian Open, Wimbledon da kuma US Open.

"Na ji dadi matuka," a cewar dan wasan mai shekaru 24, wanda ya sha kayi sau biyu kacal a wasanni 66 da ya buga a bana. "Na taka rawar gani a bana, kuma ina ci gaba da haskakawa. Koda yaushe na kara da Rafa ina jin jiki.

"Ya taka rawar gani a wannan gasar, ina so a ce muna da sauran wasanni a shekaru masu zuwa."

Nadal ya doke Djokovic a wannan mataki watanni 12 da suka gabata, amma yanzu ya sauya waccan nasara bayan da ya doke dan kasar ta Spain.