Ba Ferdinand da Vidic a wasan Man U da Benfica

Rio Ferdinand
Image caption Wasanni biyu kawai Ferdinand ya buga a Premier bana

Babu Rio Ferdinand a tawagar Manchester United zuwa Portugal domin fafatawa a wasan da United din za ta yi da Benfica a gasar zakarun Turai ranar Laraba.

Ba a zaton Ferdinand ya samu sabon rauni - illa dai kawai an hutar da shi ne bayan da ya taka leda har ta minti 90 ranar Asabar a karon farko a kakar bana.

Ganin cewa Nemanja Vidic ba zai taka leda a wasan ba, Jonny Evans ne ake saran zai buga tare da Phil Jones.

Akwai dai Michael Owen a tawagar. Sai dai babu Mame Biram Diouf da Federico Macheda.

Duk da cewa Ferdinand da Vidic ne kan gaba a bayan United, babu alamun United na fuskantar matsala game da rashin lafiyarsu - duka Ferdinand da Vidic na fama da rauni daban-daban.

A rashin na su dai, Evans da Jones ne ke rike bayan, kuma kwallaye uku kawai aka zira musu a wasanni hudu inda kuma suke kan gaba a teburin gasar Premier.