Siasia ya ce makomar Enyeama na ga NFF

Image caption Kocin Najeriya, Samson Siasia

Kocin Najeriya, Samson Siasia ya ce ya amince da hakurin da mai tsaron gidan Super Eagles, Vincent Enyeama ya bada bayan hargitsin da ya tada tsakanin 'yan wasan kasar kafin sun tafi Madagascar.

Har wa yau dai Siasia ya kara da cewa makomar Enyeama a tawagar Super Eagles na hannun Hukumar kula da kwallon Najeriya ta NFF.

Tuni dai Enyeama ya bada hakuri kan abun da ya faru, wanda kuma ya yi sanadiyar cire shi cikin jerin 'yan wasan da suka taka leda a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika da kasar ta buga da Madagascar.

A wasan sadan zumunci ma da kasar ta buga da Argentina, ba'a gayyaci dan wasan ba.

Siasia dai yace saboda rashin da'ar da dan wasan ya nuna Hukumar NFF ta dauki matakin ladabtar da shi, kuma itace kawai za ta iya bada izinin a dawo da shi cikin tawagar kasar.