Sion ba ta yi nasara a daukaka karar da ta yi ba

Hakkin mallakar hoto scotland
Image caption Wasan Celtic da FC Scion

Kungiyar Sion ba ta yi nasara ba a daukaka karar da tayi zuwa Uefa ba kan a maida kungiyar Celtic da aka yi cikin sahun kungiyoyin da za su taka leda a gasar Europa.

Celtic dai a yanzu haka za ta taka leda ne da Atletico Madrid a ranar alhamis a gasar zakarun Turai.

Sion dai ta tsallake domin taka leda a gasar Europa, bayan ta doke Celtic da ci uku da guda a wasan share fage.

Uefa dai ta hana Sion taka leda a gasar ne saboda ta yi amfani da 'yan wasan da basu dace ba.

A yanzu haka dai akwai yiwuwar kungiyar ta shigar da kara a kotun daukaka karar wasanni ta duniya.