Blatter ya musanta cewa ya kulla yarjejeniya da Platini

Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya musanta cewa akwai yarjejeniya dake tsakaninsa da Shugaban Uefa Platini, domin ya sauka masa daga kujerar Fifa a shekarar 2013.

Rahotanni dai na nuni da cewa Blatter na iya sauka a shekara ta 2013, kafi wa'adinsa ya cika a shekarar 2015.

Amma Blatter ya rubuta a shafinsa na twitter cewa: "Babu wata yarjejeniya da na kulla da Michel Platini cewa zan saukan masa daga kujera na, wannan batu bashi da tushe."

Blatter, mai shekarun haihuwa 75, ya kara cin zabe ne bayan ya tsaya shi kadai a watan Yuni.

Abokin takararsa Mohamed Bin Hammam, Shugaban Hukumar kwallon kafa na nahiyar Asiya, ya janye ne daga takarar, bayan an zarge shi da bada cin hanci a lokacin da yake yakin neman zabe.