Man City za ta haskaka a gasar zakarun Turai- Mancini

Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini ya amince cewa 'yan wasansa ba su taka leda ba da kwarin gwiwa a wasan farko da su ka buga a gasar zakarun, inda kuma ya ce ya yi amanar cewa kungiyar za ta haskaka nan gaba a gasar.

City dai ta samu maki guda ne bayan ta buga kunnen doki da Napoli, inda su ka tashi daya da daya.

Mancini ya ce: "A wurin mu, wannan wasa ne mai mahimmanci, ina ganin saboda haka ne 'yan wasan suka sa fargaba a zuciyarsu a wasan."

Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa a wasan da kungiyar za ta buga da Bayern Munich, za ta taka rawar gani.

Mancini ya kara da cewa: "Wannan ce gasar zakarun Turai ta farko da muka halarta, saboda haka 'yan wasansu suna so suyi nasara, shine kuma yasa kowa a cikinsu naso ya zura kwallo."