'Yan wasan tawagar Ethopia 15 sun bace a Mozambique

Hakkin mallakar hoto caa
Image caption 'Yan wasan tawagar Ethopia

Jami'an tsaro a kasar Mozambique sun ce 'yan wasa 15 daga cikin tawagar Ethopia sun bace daga masaukin 'yan wasa na gasar wasannin Afrika da ake yi a kasar.

Ba dai sabon abu bane bacewar 'yan wasan domin a baya ma, 'yan wasan Ethopia sun sha tserewa a manyan gasar wasannin duniya, musamman ma a Turai da kuma Amurka.

Abun mamaki anan shi ne yadda 'yan wasan suka bace a Mozambique, ganin cewa kasar ma na fuskantar matsin tattalin arziki kamar Ethopia.

Amma Mozambique din dai wata mafaka ce da za'a iya bi zuwa kasar Afrika ta kudu.

Daya daga cikin masu horon 'yan tseren Ethopia ya tabbatarwa BBC bacewar 'yan wasan kuma ya ce akwai yiwuwar suna kan hanyarsu zuwa kasar Afrika ta kudu.

Kwamitin shirya gasar wasanni na Afrika ya ce babu abun da za su iya yi domin hana 'yan wasa sauya kasar haihuwa.

'Yan sanda dai na ci gaba da bincike amma babu wanda ke sa ran za'a gano inda 'yan wasan su ke.