Muna son David Beckham - Leonardo

david Beckham Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Beckham yana taka leda ne a LA Galaxy

Daraktan wasanni na Paris Saint-Germain Leonardo ya bayyana cewa yana son David Beckham domin ya taka leda a kulob din.

Leonardo ya shaida wa BBC cewa: "Na yi aiki tare da shi a AC Milan inda Beckham dan shekaru 36 ya je a matsayin aro daga kungiyar Amurka ta LA Galaxy, kuma muna da kyakkyawar fahimta.

"Ba karamin mutum ba ne, ya fi karfin dan kwallo kawai, amma koda yaushe yana horo kuma yana buga kwallo kamar saurayi.

"Mutum ne da nake girmamawa kuma yana burge ni sosai - game da duk abinda ya ke yi a kwallon kafa."

Lokacin da aka tambaye shi ko kulob din na Qatar na duba yiwuwar sayen tsohon kyaftin din na Ingila, Leonardo ya ce: "Kofa a bude ta ke.

"Yana da nutsuwa, sauraro da kuma ganin an samu nasara a koda yaushe. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa na ke matukar kaunarsa".