AAG: Ghana da Kamaru sun lashe zinari a kwallon kafa

Image caption Babbar Tawagar Ghana

Tawagar Mazan Ghana na kwallon kafa ta doke na Afrika ta kudu da ci hudu da biyu a bugun fenarity a wasan karshe da kasashen biyu su ka buga a gasar wasanni ta Afrika.

Kasashen biyu dai sun buga kunnen doki ne a cikin lokaci da karin lokaci.

A bangaren mata kuwa, tawagar Kamaru ce ta doke Ghana da ci daya mai ban haushi a wasan karshe.

Wannan ne dai karo na farko da kamaru ta lashe zinari a wasan karshe a gasar wasanni ta Afrika.

Madeleine Mani Ngono ne ta zura kwallon ana minti 56 da wasan.