Man United ta doke Chelsea a Old Trafford

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wayne Rooney yana murnar zura kwallo

Manchester United ta ci gaba da haskakawa a gasar Premier ta Ingila, inda ta doke Chelsea da ci uku da guda a filin wasa na Old Trafford.

Chris Smalling ne ya fara zura kwallo a ragar Chelsea ana minti takwas da fara wasan.

Daga baya ne kuma Nani da Rooney suka kara kwallaye biyu, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ana dawowa ne kuma Fernando Torres ya fanshe kwallo guda, inda wasan ya kuma uku da guda, amma sai United ta samu fenarity, wanda kuma Rooney ya barar.

Shima dai Torres ya samu wata dama, bayan ya zare mai tsaron gidan Manchester United, amma ya kaso zura kwallo a raga.

A yanzu haka dai Manchester United ce ke jan ragama a gasar ta Premier.