Davis Cup: Argentina ta kai wasan karse

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Djokovic na fama da ciwon baya

Dan wasan Tennis din Serbia Novak Djokovic ya fice daga wasan da kasar ke bugawa da Argentina saboda rauni a gasar Davis Cup.

Juan Martin del Potro wanda ya bugawa Argentina ya lashe wasan ne da ci uku da guda.

Djokovic dai ya daina buga wasan ne a lokacin da del Portrp ke kan gaba da maki 6-7 0-3.

Argentina za ta garzaya Spaniya ne a watan Disamba domin buga wasan karshe da kasar bayan Rafeal Nadal ya taimaka mata a nasarar da ta yi akan Faransa da ci hudu da guda.