Tottenham ta lallasa Liverpool da 4-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adebayor ya zura kwallaye biyu a wasan

Liverpool ta kare da 'yan wasan tara a wasan da Tottenham ta lallasa ta da ci hudu da nema a filin White Hart Lane a gasar Premier ta Ingila.

Emmanuel Adebayor ya zura kwallaye biyu a wasan, a yayinda Luka Modric da Jermain Defoe, kowannen su ya zura kwallo guda.

An dai sallami 'yan wasan Liverpool Charlie Adam da kuma Martin Skrtel a wasan.

A yanzu haka dai Liverpool ta sha kashi ne a wasanni biyu da ta buga a jere a gasar ta Premier.