Ferguson ya soki tadewar da Cole ya yiwa Hernandez

Image caption Kocin United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya soki tadewar da dan wasan Chelsea Ashley Cole ya yiwa Hernandez a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a gasar Premier.

Javier Hernandez ba zai taka leda ba na tsawon makwanni biyu saboda raunin da ya samu.

Ferguson ya shaidawa MUTV cewa: "Gaskiya tadewar na fitan hankali ne. Ashley ya yi ganganci."

"Bamu san yadda Hernandez zai kasance ba. Kafarsa ta sandare."

Ferguson ya kuma yi tambaya kan dalilan da yasa ba'a ba kungiyar fenarity ba, bayan da aka nunawa Cole katin gargadi a wasan.

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya kare Cole inda ya ce dan wasan bai kai harin bane da gangan.