Muna bukatar karin 'yan tsakiya - Mancini

Roberto Mancini
Image caption Man City ta kashe kudi wajen sayen 'yan wasa

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce ba shi da isassun 'yan wasan tsakiya a tawagarsa.

An fara dukkan wasannin bana da Yaya Toure yayin da wasa daya ne kacal aka buga babu Gareth Barry.

James Milner da Nigel De Jong suna fama da rauni, yayin da Owen Hargreaves bai gama murmurewa ba.

Don haka Mancini ya ce: "Muna karancin 'yan tsakiya, saboda mutane biyu na fama da rauni. Ba ni da 'yan wasa. 'Yan baya kawai na ke iya sauyawa."

Mancini na da isassun 'yan wasan gaba inda David Silva da Samir Nasri ke haskakawa, sannan Adam Johnson ke jiran ko-ta-kwana a benci.