Redknapp na son Modric ya kulla sabuwar yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham, Harry Redknapp yana son shugaban kungiyar Daniel Levy ya fara tattaunawa da Luka Modric game da wata sabuwar kwantaragi.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 26 ya nuna karara cewa yana son ya koma Chelsea a farkon kakar wasan bana, amma kungiyar taki amincewa da tayin fam miliyan 40 da aka yi masa.

Bayan kwallon da dan wasan ya zura ne a nasarar da tayi a kan Liverpool ne ya sa Redknapp ya ce; " Abun da ya sa kenan aka yi mashi tayin fam miliyan 40.

"Ina ganin shugaban kungiyar zai tattauna da shi game da kulla sabuwar yarjejeniya."