'Yan wasan Tennis na tunanin yajin aiki- Murray

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Dan wasan Tennis din Burtaniya, Andy Murray ya ce manyan 'yan wasan Tennis na duba yiwuwar shiga yajin aiki, idan ba'a duba lokutan da ake shirya manyan gasa ba.

'Yan wasan Tennis dai na nuna rashin dadin game da yadda ake cakude wasanni babu hutu, abun da kuma ke sa su gajiya.

'Yan wasan dai za su gana a birnin Shanghai na kasar China domin tattauna makowarsu.

Murray ya shaidawa BBC cewa: "Akwai yiwuwar mu shiga yajin aiki. Na tattauna da wasu 'yan wasa kuma sun nuna mun cewa basa fargabar shiga yajin aiki."

Ya ce kan 'yan wasan a hada yake domin samowa kansu sauki.