Villas- Boas ya nuna kwarin gwiwa akan Torres

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya nuna kwarin gwiwa akan Fernando Torres, bayan dan wasan ya barar da kwallo a kashin da kungiyar ta sha a hannun Manchester United da ci uku da guda.

Kocin Chelsea dai ya nace cewa kungiyar za ta yi takarar lashe gasar Premier duk da kashin da tasha a hannun United.

Torres dai ya zura kwallonsa na farko a wasan, kafin ya barar da kwallon bayan ya tsame mai tsaron gidan Manchester United David de Gea.

Villas-Boas dai ya ce dan wasan ya taka rawar gani kuma yana ganin nan gaba zai haskaka.