Daniel Agger zai yi jinya na tsawon wata guda

Dan wasan bayan Liverpool, Daniel Agger ba zai taka leda ba na tsawon makwanni hudu saboda raunin da ya samu a hakarkarinsa, bayan kashin da kungiyarshi ta sha a hannun Tottenham a karshen mako.

Dan wasan ya yi mumunar faduwa ne, abun da kuma yasa aka sauya shi kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya ce: "Dalglish ya samu karaya a hakarkarinsa, kuma yana fsukantar matsala."

Agent din dan wasan ya ce yana cikin wani hali, saboda ya karya kasusuwa biyu a hakarkarinsa, kuma dolene ya yi jinya na tsawon makwanni hudu.