Javier Hernandez zai dawo horo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Javier Hernandez

Dan wasan Manchester United Javier Hernandez zai dawo horo a ranar Laraba, bayan raunin da ya samu a nasarar da kungiyarsa tayi akan Chelsea a ranar Lahadi.

An dai sauya dan wasan ne bayan wata mumurnar tadewa da Ashley Cole ya yi masa a wasan.

Agent din dam wasan Eduardo Hernandez ya ce raunin bai yi muni ba, kafarsa ta kumbura ne kawai.

"Zai fara horo ba tare da wani matsala ba a ranar Laraba."