Hukumar IOC na binciken Issa Hayatou

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Hukumar Caf, Issa Hayatou

Kwamitin da'a na Hukumar shirya wasanni Olympic IOC na binciken shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika Caf, Issa Hayatou kan zargin cin hanci.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta nada Issa Hayatou ne a matsayin wanda zai jagoranci harkar kwallon kafa a gasar Olympic din da za'a shirya a badi a Landan.

"Kwamitin da'a na zaman kansa ne, kuma a yanzu haka muna bincike." In ji Kakakin IOC.

Hayatou ya musanta zargin da shirin talbijin na BBC ya yi masa na karbar cin hancin dalan Amurka dubu ashirin daga wani kamfanin kasuwanci da kewa Fifa aiki a shekarun 1990's.

Ya nace cewa kudin da ya karba anyi amfani da su ne wajen bikin ciki shekaru arba'in da Caf ta yi.