Inter Milan ta sallami kocinta Gasperini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gian Piero Gasperini

Inter Milan ta sallami kocinta Gian Piero Gasperini bayan watanni uku da fara aiki da kungiyar.

Kocin mai shekarun haihuwa 53, ya sha kashi a wasanni hudu cikin biyar da ya buga a gasar Serie A ta Italiya, a yayinda ya samu maki daya a wasan da ya buga da Roma.

A yanzu haka dai kungiyar ce ta 17 a tebur a gasar Serie A.

Kashin da kungiyar ta sha da yafi muni shine wadda Novara ta doke ta da ci uku da daya.

Har wa yau Inter ta sha kashi a hannun Trabzonspor da ci daya da nema a filin San Siro a gasar zakarun Turai kuma AC Milan ma ta doke ta a gasar Italiyan Super Cup a watan Agusta.

Gasperini ya maye gurbin Leonardo ne wanda ya koma kungiyar Paris Saint-Germain a Faransa.