'Ina da karin shekaru a harkar tamoula'- Owen

Image caption Micheal Owen

Dan wasan Manchester United, Michael Owen ya jaddada cewa, yana da karin shekaru a harkar tamoula, bayan rawar da ya taka a wasan da Kungiyar ta doke Leeds a gasar cin kofin Carling.

Dan wasan dai, ba ko da yaushe yake takawa United leda ba a gasar Premier, amma ya ce yana da rawar da zai taka a kungiyar bayan kwallaye biyun da ya zura a nasarar da kungiyar ta yi da ci uku da nema.

"Shekaru na 31, ina da karin wasu shekaru a harkar tamoula." In ji Owen.

"Akwai matsin lamba inda ba'a bana samu taka leda a koda yaushe a kungiyar."

Ya kara da cewa: "Shiyasa duk sanda aka ce in buga, nake nuna kwazo ne, saboda ba koda yaushe ake bani dama ba."