Wenger na son kara shekaru 14 a Arsenal

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce bai girgiza ba ko kudan game da matsin lambar da yake fuskanta a yayinda ya ce yana so ya jagoranci kungiyar na tsawon lokaci.

Ana dai sukar kocin saboda matsayin 17 da kungiyar ta ke a gasar Premier, da kuma yadda ya siyar da wasu manyan 'yan wasan kungiyar a bana.

Amma bayan nasarar da kungiyar ta samu akan Shrewsbury da ci 3-1 a gasar cin kofin Carling, Wenger ya ce: " Suratan da ake yi a kaina bai dame ni ba, ko kadan.

"Na kai shekarun 14 hudu a wannan kungiyar, kuma a kowace shekara sai mun buga gasar zakarun Turai. Ina son in kara wasu shekaru 14 a Arsenal."

Shugaban kungiyar Arsenal, Ivan Gazidis ya shaidawa BBC cewa kungiyar ba ta tunanin sallaman kocin.